Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya kaddamar da rabon naira miliyan 100 a matsayin basi da babu ruwa ga malamai Wadanda ke aiki a karkashin Hukumar Ilimin Firamare ta kano (SUBEB) a fadin jihar.
Da yake Mika chekin kudaden ga Malaman amadadin Mai girma Gwamna Abba Kabir yusuf a hedikwatar SUBEB da ranar Laraba, Kwamishinan Ilimi na Jihar Kano, Gwani Dr. Ali Haruna Makoda,, Wanda ya Wakilci Gwamnan, ya ce Gwamna Yusuf ya amince da bayar da wannan lamuni na naira miliyan 100 ga malamai karkashin SUBEB, tare da kokarin ci gaba da Bunkasa walwalar Malama da horas da su lokaci zuwa lokaci domin cika burin kowane malami da suke kulawa da tarbiyyar dalibai.
Ya Kuma yabawa shugabannin kananan hukumomin jahar kano bisa yadda suke kokari wajen talafawa cigaban Ilimi a jahar Kano.
Tun da farko Shugaban Hukumar SUBEB ta Jihar Kano, Alhaji Yusuf Kabir, ya yabawa gwamnatin jihar bisa kokarin da take yi wajen kare fannin ilimi.
Yace Malamai dubu daya da Dari biyu da shida ne suka amfana da wannan tallafin lamunin.
Alhaji Yusuf Kabir ya yaba da jajircewar gwamnatin Alhaji Abba Kabir Yusuf wajen daukar matakan da suka dace domin ceto harkar ilimi.
Sai ya tabbatar wa da Kwamishinan cewa za a raba kayan zuwa makarantu yadda aka tsara domin tabbatar an yi amfani da su yadda ya kamata.
Wasu daga malaman da suka amfana sun bayyana Jin dadi tare da yabawa gwamnatin jahar kano