‘mijin Taslim wato Alh. Nasiru Buba wanda ya shigar da karar dakataccen kwamishinan aiyuka na musamman na gwamnatin jahar Jigawa Alh. Auwalu Danladi Sankara bisa zargin mu’amala da matarsa Taslim ya koka bisa yanda ofishin mataimakin babban sifeton yan sanda na kasa mai kula da shiyya ta daya dake nan kano ya gabatarwa babbar kotun shari’ar musulunci ta kofar Kudu rahoton bincike akan abin da ya faru ba tare da shaidun hotuna da muryoyi da kuma video fiye da 850 da ya gabatarwa ofishin ba.
A yayin da yake ganawa da manema labarai Alh. Nasiru Buba ya yi mamaki matuka akan yanda kotu ta wanke Alh. Auwalu Danladi Sankara ba tare da an sanar da su zaman kotun ba wadda hakan ta sa yake zargin akwai rufa rufa da kudundune a cikin rahotan.
Ya ce duk da kotun na da damar yanke hukuncin bisa shawarar babban lauyan gwamnati amma rashin gayyatarsa ko lauyansa zaman kotun ya sa yana shakku akan sahihancin binciken da rashin ba shi damar ji daga bangaren sa kafin yanke hukuncin.
A nasa bangaren lauyansa Br. Rabi’u M. Sidi ya tabbatar da cewa babu wanda ya gayyace su zaman kotun.
Ya ce a bisa tsarin Shari’ah wanda ya shigar da kara kai tsaye sai an nemi ji daga bangarensa kafin a yanke hukunci.
Br. Rabi’u Sidi wanda yi mamaki da wanke Auwalu Sankara ya ce ba su gamsu da hukuncin kotun ba adon haka za su tattauna da mai kara domin fitar da matsaya akan daukar mataki na gaba.
Idan za a iya tunawa a jiya Litinin alkalin babbar kotun shari’ar musulunci ta dake kofar kudi Shek Ibrahim Sarki Yola ya wanke dakataccen kwamishinan aiyuka na jahar Jigawa Alh. Auwalu Danladi Sankara akan zargin badala da matar aure Taslim bisa la’akari da rahoton bincike da ofishin mataimakin babban sufeton yan sanda shiyya ta daya dake nan kano ya gabatar masa inda ya ce ya nuna babu kwararan hujjoji dake nuna ya paikata hakan.
Credit: Nura Bala Ajingi