Shugaban Karamar Hukuma Makoda Alhaji Auwalu A. Isah ne ya bayyana haka a jawabinsa yau yayain daya Jagoranci Tattakin wayar dakai don kira ga iyayen yara susa yaransu a Makaranta domin Samun Ilmin Addini dana Zamani.
Shugaban wanda Hon. Unar Isah Tukui Shugaban Majalisar Kansiloli na Karamar Hukumar Makoda ya wakilta ya bayyana cewa wannan Tattakin wanda aka gudanar a Garin Koguna Shedkwatar Mulki ta Karamar Hukumar Makoda za’a gudanar da Makamancinsa a Mazabun yankin.
Daga karshe Shugaban Karamar Hukumar ta Makoda ya jaddada aniyar Gwamnatinsa na tainakawa Ilmi, ya kuma bukaci zababbun Kansiloli dasu shiga cikin Gangamin wajan aiwatar da Makamancinsa a Mazabunsu.
Da yake jawabi yayin fara tattakin Sakataren Ilmi na Karamar Hukumar Makoda Mal Mijitapha Umar Yunusa ya bayyana cewa bayan taron wayar dakai daya gabata kwanakin baya, Kungoyin da suke bada Tallafi na Duniya E.U da UNICEF karkashin Shirinnan na EYE Project ne ake gudanar da Gangamin a Kananan Hukumomi 10 na Jihar Kano Makoda tana cikinsu.
Sakataren ya kara da cewa Karamar Hukumar Makoda ta Gudanar da wannan Tattaki da nufin Kara wayar dakan Al’ummar yankin.
A karshen Jawabinsa Sakataren Ilmin ya kuma bukaci Gudummawar Zababben Shugaban Karamar Hukumar Alhaji Auwalu A. Isah da Kansilolinsa wadanda daman gata ne ga Ilmi a Yankin, gami da Masarauta, Limamai da Shauran Masu Ruwa da Tsaki dasu tallafawa kokarin Hukumar Ilmin Bai daya wajan wayar dakan Al”umma akan Mahimmanci sanya yara a Makaranta.
A jawabansu daban daban Shugaban Kwamitin Ilmi na Karamar Hukumar Makoda Alhaji Haruna Isyaku Makoda, Shugaban Kungiyar Al’umma Gatan Makaranta Mal. Hamisu Garba da Shugaban Kungiyar Malamai da Iyayen Yara ta Karamar Hukumar Makoda Mal. Tanimu Lawan Makoda sun yabawa kokarin Kungoyoyin Biyu bisa Bibiya da Sa”ido da sukeyi akan Ilmin Yara da kuma daukar nauyin wannan
Gangami da nufin wayar dakan Al’umma.
Shugabannin Kungiyoyin sun kuma bada tabbacin bada Gudummawar da ake bukata wajan Magance wannan Matsala ta rashin sanya Yara a Makaranta.
An fara Tattakin cikin Aminci daga daga Harabar Hukumar Ilmin Bai Daya ta Karamar Hukumar Makoda zuwa Cikin Garin Koguna,
Tattakin ya sami Halartar Dukkannin Shugabannin Sassa da Shauran Ma’aikan Hukumar Ilmin Bai daya ta Makoda, Shugabannin Makarantun Firamare dana Sikandire, Kungiyoyin Harkokin Ilmi da Shauran Masu Ruwa da Tsaki akan Harkar Ilmi, da Jami’an Tsaro na Karamar Hukumar Makoda.