Acigaba da gabatar da alluran riga kafin cututtukan kananan yara masu kassara su. Karamar hukumar Rimin Gado ta samu nasarar yiwa yara alluran riga kafin, sama da yara dubu arba’in da hudu (44,000) acikin yini uku(3) kacal ba tare da samun wata tangarda ba.

IMG 20241105 WA0093

Sanarwar ta fito ne daga jami’in yada labarai na Karamar hukumar Rimin/Gado Garba Bello.

Shugaban sashin lafiya a matakin farko Alhaji Salisu Umar ne ya ambata hakan, lokacin da ‘yan kwamatin kar ta kwana suke sauraren yadda aka gudanar da alluran riga kafin a wannan yinin.
Alhaji Salisu Umar yace waje daya ne aka sami matsala,kuma nan take ya bada umarnin zuwa dan a gyara.
Shugaban karamar hukumar Rimin Gado Alhaji Salisu Umar Jili ya yaba da irin kokarin da ma’aikatan lafiyar suke yi, sannan ya nemi da su kara jajurcewa wajen kawar da cututtukan da suke addabar yaran.

Daraktan mulki Injiniya Aminu Sharif Kabara ya godewa iyayen da suke barin matayensu zuwa wajen karbar riga kafin.
Injiniya Aminu Sharif Kabara ya tunatar da iyaye maza irin muhimmanci alluran riga kafin na yau da kullum, dan haka ya roke su,da su kyale iyaye mata da su dinga kai yaran su Asibiti dan yiwa yaran su riga kafin.


Uban kasa hakimin Rimin Gado sarkin shanun Kano Alhaji Shehu Muhammad Dan Kadai ya jinjinawa Dagatansa da masu unguwannin sa, saboda irin kokarin da suke bayarwa kamar yadda aka umarce su.

Sannan yayi kira ga al’ umar yankin da su cigaba da bawa Jami’an lafiya hadin kai wajen gudanar da rigakafin a lokacin da aikin ya ta taso.

 

Share.
Leave A Reply Cancel Reply

Exit mobile version