Gidauniyar Dr Aminu Magashi Garba a jiya ta gudanar da taron Shan ruwa GA masu ruwa da tsaki a fadin jahar nan.

A yayin da ya ke jawabin maraba Dr Magashi ya bayyana farin cikin sa na muhimmancin Ranar ta kungiyoyi masu Zaman Kansu.

Inda ya bada takaitaccen tarihin kafuwar kNet a shekarar dubu biyu da biyu inda aka Kai ta Kai kawon tattaunawa da kungiyoyi daban daban har aka haifar da gamaiyyar kungiyoyi masu Zaman Kan su daga bisa ni shine aka Samar da ofishin NGO a lokacin mulki tsohon gwamnan Kano senator rabiu Musa kwankwaso da kuma inda shima tsohon Gwamna malam Ibrahim shekaru ya cigaba da sahalewar ofishin.

Ana sa jawabin Mai bawa gwamna shawara ta musaman Kan kungiyoyi masu Zaman Kan su Hon. Nasiru Isa Dikko (Jarma), ya bayyana yanda su Ka jajrice har aka samu kafuwar ofishin kungiyoyi masu Zaman Kansu a jahar nan inda ya ce yin riko da gaskia da amma shine ya sa Dr Aminu Magashi Garba yayi fice a bangaren kungiyoyi masu Zaman Kan su.

Ya kuma ja hankalin sababbin shugabannin ƙungiyar kNet (kano network of Ngo) da su yi koyi da Dr Aminu Magashi bisa jajircewar sa a kodayaushe.

Ana ta jawabin Dr. Maryam Nasir, CEO Anatomia Ltd & Coordinator, WORE ta taya sababbin shugabannin na kNet murna ta kuma jahankalin su da su hada Kai wajen aiwatar da aikin su domin Rashin jituwa na jawo nakkasu ga cigaban kungiyoyi a jahar nan.

Share.
Leave A Reply Cancel Reply

Exit mobile version