Masu zuba jari da ke shirye su yi hadin gwiwa da Gwamnatin Jihar Kano wajen ayyukan hakar ma’adanai an ba su tabbacin kariya yayin da suke jihar.A

cikin wata sanarwa da daraktan wayar da kan jama’a na ma’aikatar ma’adanai da albarkatun kasa Adamu dabo dawakin/tofa ya raba wa manema labarai, ya ce kwamishinan ma’aikatar ma’adanai da albarkatun kasa Alhaji Safiyanu Hamza Kachako ya bayyana hakan a ranar Laraba yayin da yake karbar bakuncin Manajan Daraktan Kamfanin hakar ma’adinai na kasar Sin, Mista Alex Zhang. Kwamishinan ya bayyana cewa ‘yan kasashen waje da ‘yan Najeriya da ke son hada kai da gwamnatin jihar domin kafa masana’antun hakar ma’adinai a cikin jihar za su samu kyakkyawan yanayi na gudanar da ayyukansu.

1000715949

Ya kuma nanata kudurinsa na nuna yanayi mai inganci da daidaiton alaka ta aiki tare da irin wadannan masu zuba jari da nufin samar da guraben ayyukan yi, inganta kudaden shiga na cikin gida, da ci gaban al’umma da kuma kare muhalli daga lalacewa sakamakon ayyukan masana’antu.

Manajan Daraktan Kamfanin Zarthwish, Mista Alex Zhang, ya nuna jin dadinsa da kyakkyawar tarba da Kwamishinan ya yi masa, ya kuma nuna kyakkyawan fata tare da nuna musu dimbin ma’adanai daban-daban a Kano sannan ya nuna jin dadinsa bisa la’akari da nau’in dakin gwaje-gwajen dake jahar.

Daraktan Binciken Harkar Ma’adanai, Alhaji Muhammad Bala a yayin taron tattaunawa, Mr. Alex Zhang ya yi alkawarin yin nazarin tayin da Kwamishinan ya yi a tsanake tare da yin nazari a kan wane fanni na aikin hakar ma’adinai, kamfaninsa zai hada gwiwa da gwamnatin jihar Kano domin cimma burin da aka sa a gaba.

 

Share.
Leave A Reply Cancel Reply

Exit mobile version