KIMANIN YARA DALIBAI TALATIN DA BIYU NE DAGA MAKARANTAR ISLAMIYYA TA USMAN BIN AFFAN DAKE GARIN DAU NA YANKIN KARAMAR HUKUMAR WARAWA SUKAYI NASARAR SAUKAR KARATUN ALKUR’ANI MAI GIRMA.
SHUGABAN KARAMAR HUKUMAR WARAWA, ALHAJI LAMIDO SUNUSI AHMAD GARIN DAU YA NUNA GAMSUWA DA FARIN CIKI BISA YADDA YARA DALIBAN SUKE DA KISHIN ILIMIN ADDININ ISLAMA A ZUKATANSU.
ALHAJI LAMIDO SUNUSI AHMAD YA JADDADA KUDIRIN MAJALISSAR KARAMAR HUKUMAR WARAWA NA CIGABA DA TALLAFAWA HARKOKIN ILIMIN ADDININ MUSULUNCI, YA TAYA DALIBAN MURNA TARE DA JAN HANKALIN SU FADADA NEMAN ILIMI.
ANASA BANGAREN KANSILAN MAZABAR GARIN DAU, ALlH.ABUBAKAR SADIQ NUHU YA BADA TABBACINSA NA BIJIRO DA TSARIN TAIMAKAWA MAKARANTUN ALLO DANA ISLAMIYYA, TARE DA TAYA MURNA GA DALIBAN.
SHUGABAN MAKARANTAR USMAN BIN AFFAN GARIN DAU, MALAM BASHIR MUHD YAYI JAWABI KAN TARIHIN KAFUWAR MAKARANTAR TARE DA JAN HANKALIN IYAYE DASU BADA HADIN ΚΑΙ GA IYAYE DALIBAI SU RINKA TULAWA.
AMADADIN DALIBAN, FATIMA ADAM ISAH DA UMAR ABUBAKAR SURAJ SUN GODEWA MALAMAI DA IYAYE BISA NASARAR DA SUKA SAMU TA SAUKA.