Fitaccen Mallami yayi Kira GA Musulmai su dage wajen ribatar Watan karshen Azumin Ramadan

Sa hannu Salisu Kassim Yakasai, jami’in Sashen Yada Labarai da Hulda da jama’a.

An shawarci al’ummar Musulmi a jihar nan da su kara mayar da hankali wajen kusantar Allah a cikin goman karshe na watan azumin Ramadan.

Wannan kira ya fito ne daga bakin Sheikh Muhammad Sunusi Bamalli yayin rufe karatun Alƙur’ani mai girma da Tafsiri karo na she Kara 22, wanda aka gudanar a makarantar da marigayi Malam Bamalli Nuhu Yakasai ya kafa, da ke cikin karamar hukumar birni.

Sheikh din, wanda ya gudunar da tafsir yana maja bai Malam Ali Sufi, ya bayyana cewa wannan shi ne hattamar Alƙur’ani ta sauka biyar cikin shekara a shirin da biyu  da aka samu nasarar gudanarwa tare da daliban makarantar. Ya kara da cewa shirin ya kasance wata dama ta fadakar da al’umma kan yadda Musulmi zai nemi gafarar Allah tare da shirin fuskantar Ranar Alƙiyama.

Anasa jawabin, Kwamishinan  na daya a Hukumar Shari’a ta Jihar, Sheikh Malam Hadi Gwani Yakasai, ya yi bayanin muhimmancin girmama da martaba Annabi Muhammad (SAW) a matsayin fiyayyen halittar Allah, yana mai cewa yin hakan yana taimakawa wajen kare mumini daga azabar Allah.

Daga cikin manyan baki da suka halarci taron akwai Farfesa Kamilu Sani Fagge da Farfesa Ashiru Aminu  Bakafusi Yakasai, wadanda suka ja hankalin matasa da su guji dabi’u marasa kyau da kuma shaye-shaye, domin daga cikinsu ne ake samun shugabanni nagari a nan gaba.

A jawabin godiya, tsohon jakadan kasar Kuwait,  Nu’uman Hannafi Bamalli, ya yaba wa daliban makarantar kan kokarinsu da sadaukar da kai wajen hidimtawa da ci gaban makarantar.

Haka kuma an yi addu’o’i na musamman ga wasu daga cikin wadanda suka rasu da suka yi alaka da makarantar, ciki har da marigayi Alhaji Aminu Adamu Yakasai da kuma marigayi Farfesa Hafizu Miko Yakasai.

Exit mobile version