Daga Munzali Muhd Hausawa,
Daraktan Wayar da Kai,
Hukumar Kula da allunan tallace tallace ta Jihar Kano (KASA)
Hukumar Kula da allunan Tallace-Tallace da dangogin su ta Jihar Kano (KASA) ta ci gaba da shirin ta na koyon aiki da musayar ƙwarewa a Jihar Legas, inda ayyukan rana ta biyu suka mai da hankali kan hanyoyin aiwatar da dokoki.
An gudanar da wannan aikin ne tare da haɗin gwiwar ‘yar uwarta, wato Hukumar Kula da allunan Tallace-Tallace ta Jihar Legas (LASAA).
Wannan bayanin na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da Daraktan Wayar da Kai na Hukumar, Munzali Muhd Hausawa, ya sanya wa hannu.
An gudanar da aikin aiwatar da doka ne a yankin Ikoyi, musamman a titin Alakija da wasu sassan ƙaramar hukumar Ikoyi.
Yayin gudanar da aikin, Daraktan Bin Doka ana hukumar LASAA Dauda Adekola, ya bayyana cewa an samu nasara, inda aka bai wa masu gine-ginen takardun gargaɗi don tabbatar da bin doka kafin a ɗauki cikakkun matakan aiwatarwa.
Ya yaba wa Gwamnatin Jihar Kano bisa kafa wannan hukuma, yana mai jaddada cewa hakan zai taimaka sosai wajen ƙara haɓaka tushen samun kudaden shiga na jihar.
A nasa bangaren, Darakta-Janar na Hukumar KASA, Comrade Kabiru Saidu Dakata, ya bayyana cewa ziyarar koyon aiki zuwa LASAA za ta ƙara inganta ƙwarewar ma’aikatan hukumar tare da ba su damar fahimtar sabbin hanyoyin gudanar da harkokin allunan tallace tallace.
Ya nuna godiya ga shugabanci da dukkan ma’aikatan LASAA bisa kyakkyawar tarba da karamcin da suka nuna. Comrade Dakata ya kuma yi kira ga jama’a da su ci gaba da goyon bayan manufofin ci gaban Gwamna Abba Kabir Yusuf, waɗanda suka mayar da hankali kan aiwatar da muhimman ayyuka don bunƙasa jihar.

