Gov. Yusuf ya kafa sabon kwamittin binciken ta’adanci Lokacin zanga zanga watan da ta gabat

Gwamnan Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf ya kaddamar da kwamitin da zai gudanar da bincike kan ta’adin da aka yi a lokacin zanga-zangar tsadar rayuwa a jihar Kano

Da yake rantsar da wakilan kwamitin a gidan gwamnati gwamna Abba Kabir Yusuf ya hore su dasu gudanar da ayyukan su bisa gaskiya da rikon amana.

Ya bawawa wakilan kwamitin kwamitin tabbacin gwamnati ba zata yi musu katsalandan ba a yayin gudanar da aikinsu.

Ayyukan da kwamitin zai aiwatar sun hada da bincike kan wadanda ke da hannu Kan lalata dukiyar gwamnati da ta aluma wanda wasu bata gari suka jagoranta.

Kwamitin zai kasance Kar Kashin jagorancin Mai Sharia Lawal Wada Mahmoud Mai ritaya a matsayin shugaba sai Abmasada Ibrahim Wayya da ACP Mannir Madugu da Barr. Sulaiman Gezawa da kuma Reberan Murtala Mati Dangora a matsayin wakilan kwamitin.

 

 

 

 

 

 

 

Share.
Leave A Reply Cancel Reply

Exit mobile version